Would you like to receive notifications on latest updates of the following headlines?

Cikar Kwanaki 100 A Offis: Zulum Ya Gabatar Da Sakamako 77

POSTED ON September 11, 2023 •   Hausa      BY Hauwa Aliyu Balasa
Gwamnatin jihar Borno ta ce ta aiwatar da ayyuka 77, wannan na zuwa ne gab da shirye-shirye nuna wasu muhimman ayyuka a cikin kwanaki 100 a ofis da gwamnar jihar yayi. Bugu da kari kuma  wannan shine karo na biyu da Gwamna Zullun yake kan karagar mulkin jihar,Sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani, ya fitar da katin makin na kwanaki 100 a kan karagar mulki ranar Litinin a Maiduguri. A cewarsa, Zulum ya gudanar da ayyuka 10 a fannin ilimi wadanda suka hada da makarantun Mega uku, daukar malamai 4,000, gina gidajen malamai 30 da kuma biyan kudin tallafin karatu ga dalibai 14,284 a Najeriya da wasu 30 da ke karatu a kasashen waje. A fannin kiwon lafiya, sakataren gwamnatin jihar ya ce an samar da ayyuka biyar, wadanda suka hada da gina cibiyoyin kiwon lafiya guda hudu tare da kowannensu yana da karfin gadaje 30 da wuraren jinya. “Wadannan cibiyoyin kiwon lafiya su ne na matakin farko,a Limankara da ke Gwoza, Kaleri a Mafa, Zarmari a Konduga da Shuwari II a MMC, su ne wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar a ranar Juma’a. Tijjani ya kuma yi bayani kan fitar da Naira biliyan 2 domin biyan basussuka ga ma’aikatan gwamnati kuma an rubanya kudaden gratuti a duk shekara zuwa Naira biliyan 2.4 don magance koma bayan kudaden gratuti da ake bin ma’aikatan da suka yi ritaya. An kuma fitar da Naira Biliyan 1 a matsayin karin tallafi ga wadanda bala'in gobara a kasuwar Maiduguri ya rutsa da su. Dangane da ababen more rayuwa, Mista Tijjani ya ce gwamnatin ta gina tituna a cikin garin Monguno, Waka-Biu da Maiduguri, yayin da a karkashin tsaro aka samar da motocin sintiri 50 da babura 300 domin samar da kayan tsaro. “A gameda sufuri, akwai  motoci guda 30, da bas guda 25 da aka ware wa ma’aikatan gwamnati. Akwai kuma sayan kekunan lantarki guda 3,000. A kan harkar noma, akwai sayan garma da harrow guda 471 ga tararaktoci 312 da aka ware wa gamayyar kungiyoyin manoma a fadin unguwanni 312 da ke kananan hukumominmu 27. Sanarwar ta kara da cewa, “akwai kuma rabon tirela 100 na takin zamani ga manoma a fadin jihar, da kuma raba abincin dabbobi ga manoma 300 a kananan hukumomin Jere, Konduga da Mobbar.” A fannin bayar da agajin jin kai, ya ce an bayar da tallafin jin kai ga gidaje 120,000 a fadin Gwoza, Maiduguri, Jere, Kukawa, Mafa, Bama da Damboa, yayin da aka bai wa ‘yan gudun hijira 500 gidaje a Molai 500 gidaje. “Ha walau akwai niyyan cigaba da wasu ayyauka a jihar Borno da Gwamna zullum ke da muradin yi domin inganta rayuwar al'ummarsa.
0
READ ALSO
Tinubu Zai Yi Magana A Taron Kolin Yanayi Na Afirka
BY Hauwa Aliyu Balasa December 30, 2023 0

Ana sa ran shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi a yau, 5 ga Satumba, da karfe 11 na safe, yayin cikakke...

READ ALSO
Taimakon Shugaba Tinubu Wajen Nasarar Aiki Shine Burina –Yahaya Bello
BY Hauwa Aliyu Balasa September 23, 2023 0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, a ranar asabar ya bayyana cewa ba shi da wani buri a siyasance a ya...

READ ALSO
An Gurfanar Da Wasu Matasa A Kotu Bisa Zargin Tada Zaune Tsaye A Unguwar Wike
BY Hauwa Aliyu Balasa September 22, 2023 0

A ranar Juma’a ne rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu matasa uku a gaban wata kotun da ke Lugbe,...

READ ALSO
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Sa Himma Wajen Bunkasa Ilimi Cikin Gaggawa
BY Hauwa Aliyu Balasa September 21, 2023 0

A cewar Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq samar da ingantaccen ilimi ga miliyoyin yaran da...

READ ALSO
Gwamnan Kano Ya Yi Watsi Da Hukuncin Kotu Ya Garzaya Kotun Daukaka Kara
BY Hauwa Aliyu Balasa September 20, 2023 0

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ki amincewa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwa...

READ ALSO
Saudiyya Ta Ware Wa Najeriya Gurbi 95,000-Hajjin Bana
BY Hauwa Aliyu Balasa September 20, 2023 0

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, a ranar Talata ta ware wa Najeriya gurabe 95,000 don gudanar...

READ ALSO
An Hana Yan Jarida Daukan Hukuncin Zaman Kotun Karar Apc
BY Hauwa Aliyu Balasa September 20, 2023 0

A ranar Laraba ne aka hana ‘yan jarida shiga harabar kotun da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna...

READ ALSO
Argungu Gagarumar Bikin Al'adu Na Kamun Kifi
BY Hauwa Aliyu Balasa September 19, 2023 0

Bikin argungu wata hanya ce ta rayuwa ga al’ummar jihar Kebbi. Bikin yana kiyaye al'ada kuma yana i...

OUR CHANNELS:

Oyo govt. sets conditions for Sharia Court inauguration
BY Abiodun Saheed Omodara December 26, 2024 0

The Governor of Oyo State, Seyi Makinde, has said he’s aware of the move to inaugurate a Shari...


SEC promises transparency, fairness in fintech regulation
BY Abiodun Saheed Omodara December 24, 2024 0

LAGOS, Nigeria - The Securities and Exchange Commission (SEC) has assured stakeholders in the fintec...


No regret removing fuel subsidy- Tinubu
BY Abiodun Saheed Omodara December 24, 2024 0

ABUJA, Nigeria - President Bola Tinubu, on Monday, said he had no regret removing fuel subsidy. The...


Urologist cautions Nigerian men on long-term use of libido drugs
BY Abiodun Saheed Omodara December 25, 2024 0

GOMBE, Nigeria - A consultant of urologist at Federal Teaching Hospital, Gombe, Ahmed Umar, has warn...


Courts convict 742 terrorists, as 888 regain freedom
BY Benedicta Bassey December 24, 2024 0

ABUJA, Nigeria  —  The Federal Government has prosecuted not fewer than 1,743 suspec...


Approve additional consulate office in UK, US, Canada, Reps tell FG
BY Benedicta Bassey December 24, 2024 0

ABUJA, Nigeria  —  The House of Representatives Committee on Foreign Affairs has cal...


LASTMA launches technology to report traffic violations amid festivity
BY Benedicta Bassey December 24, 2024 0

LAGOS STATE, Nigeria  —  The Lagos State Traffic Management Authority has advised re...


No going back on tax reform bills - Tinubu
BY Benedicta Bassey December 24, 2024 0

LAGOS STATE, Nigeria  — President Bola Tinubu has said that there is no going back on the...


Imo governor presents 756bn budget to Assembly
BY Benedicta Bassey December 24, 2024 0

IMO STATE, Nigeria  —The Imo state Governor, Hope Uzodimma, has presented the state&rsquo...


Kogi Assembly Approves N582.4 Billion 2025 Appropriations Bill
BY Ebiakuboere England December 24, 2024 0

KOGI- The Kogi State House of Assembly has enacted the N582,404,119.489 2025 Appropriations Bill. A...


More Articles

Load more...

Menu