Would you like to receive notifications on latest updates of the following headlines?

Taimakon Shugaba Tinubu Wajen Nasarar Aiki Shine Burina –Yahaya Bello

POSTED ON September 23, 2023 •   Hausa      BY Hauwa Aliyu Balasa
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, a ranar asabar ya bayyana cewa ba shi da wani buri a siyasance a yanzu sai dai ya taimaka wa shugaba Bola Tinubu wajen samun nasara. Da yake magana game da matakin da zai dauka na gaba bayan zama gwamna, kasancewar yana daya daga cikin manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Gwamna Yahaya Bello ya yi wannan magana ne a wani taron tattaunawa da manema labarai a wajen taron GYB na shekara-shekara kuma wannan shine karo na uku wadda yake da taken 3rd Annual GYB for Nigerian Political & Crime Correspondents/Editors ranar Asabar a Abuja. Yayin da yake nuna godiya da jinjina ga Ubangiji madaukakin sarki ya ce, “Na gode wa Allah bisa nasarorin da na samu a matsayina na gwamnan Kogi,na san yadda na tarar da jihar kuma ina farin ciki da inda na kai jihar a yanzu. Kuma ina imanin cewa dan takarar jam'iyyar APC, Usman Ododo, zai gina katafaren tushe da muka shimfida wa Kogi." A cewarsa, zaben gwamnan jihar Kogi a watan Nuwamba zai kasance babbar nasara ga jam’iyyar APC domin jam’iyyar ce zata cigaba da ci a jihar Kogi haka kuma ta zo zama daram. Inda ya cigaba da cewa “Haɗin kan mu shi ya sa APC ta yi nasara a Kogi kuma za ta ci gaba da samun nasara. Jam’iyyar mu daya ce. Haka kuma akwai hanyoyin ko muce dabarun cikin gida a APC don magance matsaloli kuma a koyaushe muna amfani da hakan. Anyi kira ga yan gari da su guji fadan kabilanci koh addini domin gujewa yin haka ne zai sa a samu zaman lafiya da cigaba a jihar. Shugaban kungiyar ta NUJ ya bayyana cewa a lokutan zabukan da suka gabata na kawo kalubale da damammaki ga ‘yan jarida wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na masu sa ido kan al’umma. Daga karshe yana ƙarfafawa dukkan yan jarida da su tunkari aikin dabisa sanin ma'anar aiki, kana kuma da sanin cewa ingancin rahoto na iya yin tasiri ga makomar ƙasarmu.
0
READ ALSO
Tinubu Zai Yi Magana A Taron Kolin Yanayi Na Afirka
BY Hauwa Aliyu Balasa December 30, 2023 0

Ana sa ran shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi a yau, 5 ga Satumba, da karfe 11 na safe, yayin cikakke...

READ ALSO
Taimakon Shugaba Tinubu Wajen Nasarar Aiki Shine Burina –Yahaya Bello
BY Hauwa Aliyu Balasa September 23, 2023 0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, a ranar asabar ya bayyana cewa ba shi da wani buri a siyasance a ya...

READ ALSO
An Gurfanar Da Wasu Matasa A Kotu Bisa Zargin Tada Zaune Tsaye A Unguwar Wike
BY Hauwa Aliyu Balasa September 22, 2023 0

A ranar Juma’a ne rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu matasa uku a gaban wata kotun da ke Lugbe,...

READ ALSO
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Sa Himma Wajen Bunkasa Ilimi Cikin Gaggawa
BY Hauwa Aliyu Balasa September 21, 2023 0

A cewar Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq samar da ingantaccen ilimi ga miliyoyin yaran da...

READ ALSO
Gwamnan Kano Ya Yi Watsi Da Hukuncin Kotu Ya Garzaya Kotun Daukaka Kara
BY Hauwa Aliyu Balasa September 20, 2023 0

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ki amincewa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwa...

READ ALSO
Saudiyya Ta Ware Wa Najeriya Gurbi 95,000-Hajjin Bana
BY Hauwa Aliyu Balasa September 20, 2023 0

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, a ranar Talata ta ware wa Najeriya gurabe 95,000 don gudanar...

READ ALSO
An Hana Yan Jarida Daukan Hukuncin Zaman Kotun Karar Apc
BY Hauwa Aliyu Balasa September 20, 2023 0

A ranar Laraba ne aka hana ‘yan jarida shiga harabar kotun da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna...

READ ALSO
Argungu Gagarumar Bikin Al'adu Na Kamun Kifi
BY Hauwa Aliyu Balasa September 19, 2023 0

Bikin argungu wata hanya ce ta rayuwa ga al’ummar jihar Kebbi. Bikin yana kiyaye al'ada kuma yana i...

OUR CHANNELS:

Tackling Nigeria's Food System Crisis: Opportunities amidst Challenges
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

ABUJA, Nigeria - The Country Director of ActionAid Nigeria (AAN), Andrew Mamedu, has stated that Nig...


I Have Nothing Left, Nollywood Actress Emotional Call for Support
BY Abiodun Saheed Omodara May 15, 2025 0

A well-known Nollywood actress, Jumoke George, has publicly requested assistance, disclosing her ong...


Nasarawa Assembly Enacts Mining Bill to Ensure Compliance and Community Welfare
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

NASARAWA, Nigeria - The Nasarawa House of Assembly On Tuesday approved a mining bill aimed at regula...


UNHCR Raises Alarm over Germany's Stricter Border Controls
BY Abiodun Saheed Omodara May 15, 2025 0

The UNHCR has voiced its concerns regarding Germany's recent move to enhance border controls and den...


CBN Launched BVN Platform for Nigerians Living Abroad
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

The Central Bank of Nigeria (CBN), in partnership with the Nigeria Inter-Bank Settlement System (NIB...


CDS Urges Vigilance and Unity among Troops in Fight Against Insurgency
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

The Chief of Defence Staff (CDS), Gen. Christopher Musa, praised the troops of Operation FASAN YAMMA...


Tinubu Calls for Unified Tax System to Enhance Revenue Generation and Equity
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

ABUJA, Nigeria - President Bola Tinubu has reiterated his commitment to undertaking bold and compreh...


LASG to Introduce Flexible Rent Payment Plans for Low-Income Residents
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

LAGOS, Nigeria - The Lagos State government is in the process of finalizing a system that will allow...


PDP Leaders Reassure Members Amid Defections Ahead of 2027 Elections
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

ABUJA, Nigeria - Acting National Chairman of the People’s Democratic Party (PDP), Ambassador U...


World Bank: Tinubu’s Reforms Bringing Stability to Nigeria’s Economy
BY Abiodun Saheed Omodara May 14, 2025 0

ABUJA, Nigeria - The World Bank expressed approval of the federal government on Monday, noting that...


More Articles

Load more...

Menu