Bikin argungu wata hanya ce ta rayuwa ga al’ummar jihar Kebbi. Bikin yana kiyaye al'ada kuma yana inganta rayuwar su,ana gudanar da shi shekara-shekara kuma akan yi sa ne a watan Fabrairu kuma yana nuna ƙarshen lokacin noma da kuma lokacin kamun kifi.
Bikin ya samo asali ne da farko bisa tsarin ibada kafun aka samu sauye-sauye da gyare-gyare da dama a bikin Argungu, wanda shi ne a yau ya sa bikin ya kasance mai salo da kuma ci gaba.Shi wannan bikin kamun kifi na Argungu yana daya daga cikin manya-manyan bukukuwan da ake gudanarwa duk shekara domin kawo karshen kiyayyar da aka kwashe tarun shekaru ana yi tsakanin yankin khalifancin Sokoto da masarautar Kebbi dake arewacin Najeriya.
Abun ban sha'awar shi ne akan kwashi kwanaki hudu ana wannan taron na al'ada,haka kuma an fi yin bikin a cikin watan Fabrairu bayan kammala duk ayyukan noma a jihar.
Akan samu sama da masunta 30,000 da suke halartar wannan bikin kamun kifi na Argungu duk shekara shekara.
Babban dalilin taron bikin shi ne gasar kamun kifi da ake yi a kogin Mata Fada, inda ake amfani da gidan kamun kifi na gargajiya da aka kira shi da kwarya.
Hakan zai tabbatar da cewa kogin ba shi da tashin hankali koh fushi wajen kamun kifin, sa’anan ya kori kada da ke cikin kogin tare da gayyatar duk kifin da ke cikin kogin da ke da alaka da kogin Mata Fada. In da za a gudanar da bukin na argungu kenan .
Wani abun ban Sha’awa shi ne idan ba da izinin sarkin ruwa ba, ba za a iya kama kifi ba, domin Sarkin Ruwa shi ne mai kula da kogin Mata Fada .
Sai kuma baya ga nan duk Mai kamun kifi da ya kama kifi mafi girma zai samu kyautar da aka shirya bayarwa a shekaran,wato idan ya yi nasarar kama kifi mai nauyi sai a dora bisa sikeli.
Gwamnatin jihar Kebbi ita ta dauki nauyin bikin saboda yadda ake samun farin jini da karfin tattalin arziki a jihar ta sanadiyar wannan bikin gargajiya na Argungu.
Janar Yakubu Gowon, tare da Alhaji Diori Hammani na jamhuriyar Nijar, su ne shugabanni na farko da suka halarci bikin Argungu a shekarar 1970.
Tun daga nan ne dukkan shugabannin Tarayyar Najeriya suka fara ziyartar bikin. Gwamnonin jihohi daban-daban na kasar nan musamman gwamnonin jihohin arewa su ma su kan yi marhaban don halartar wannan taron.
Rashin zaman lafiya da karuwar matsalar ‘yan fashi da tayar da kayar baya a shekarar 2009 yasa aka dakatar da wannan biki na wani lokaci amma an sake dawo da ita a shekarar 2020 domin abubuwa sun lafa.
Bikin Argungu a halin yanzu yana daya daga cikin bukukuwan da suka shahara a Najeriya banda ma arewacin Najeriya kade harda kasashen ketere ma bikin na jan hankalin su da masu yawon bude ido a duk fadin duniya suna zuwa domin bawa idonsu abinci.