A ranar Laraba ne aka hana ‘yan jarida shiga harabar kotun da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano za ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta suka shigar a gabanta a zaben ranar 18 ga watan Maris.
A baya dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben Kano, Nasir Gawuna, ya garzaya kotu domin kalubalantar nasarar Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigeria People Party, NNPP, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben. .
Ana sa ran cewa kotun za ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC da dan takararta suka shigar a yau.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba an hana wasu ‘yan jarida shiga da suka kutsa kai cikin harabar domin sanya ido kan yadda lamarin ke gudana.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Usaini Muhammed Gumel, wanda ya zanta da Aminiya, ya ce mutane 50 ne kawai kotu ta ba da izini su shiga.
A cewarsa, “Tun a jiya muka kira sakataren kotun don jin shirye-shiryen zaman, inda suka sanar da mu cewa mutum 50 ne kawai za a bari su shiga cikin kotu”.
“Lambobin sun hada da alkalai, lauyoyin jam’iyyun biyu da mambobinsu, ‘yan jarida da kafafen yada labarai. Don haka ba ‘yan sanda ba ne suka takaita adadin.”
Har zuwa yanzu bamu samu cikakken bayanai bisa dalilin hana yan jarida shiga kotun ba.