Bikin ƙunshe yake da ayyuka masu ban sha'awa domin yadda masu dawakai ke yi wa dawakan su ado da kwalliya na zo a gani.
Yawancin lokuta ana fara bikin ne da addu’o’in Musulunci,inda za ayi wa kasa addu'a da kuma kariyar jama'a sannan a yi fareti kala-kala na sarki da tawagarsa suna bisa dawakai.
Mawaka kuwa suna tare da sarki yayinda suke masa rakiya zuwa dandalin jama'a da ke kofar fadarsa.
Baya ga hakane za a na gaisuwa yayin da dubban mayaƙan mahaya dawakai ke fafatawa a filin fareti mai ƙura da ke gaban fadar sarkin, don farawan wannan biki.
A yayin wannan fareti ne cikin dubban jama'a za a ga cewa dawakai sun sha ƙawa, an lulluɓe su cikin shagali cikin farin ciki da sirdi masu launin daban daban,sanye da gefuna na zinariya a rataye a jikin kayansu.
Mazajen kuwa da ke sanye da rawani masu kayatarwa musamman da kunne daya ko biyu a rawaninsu,zasu fito don nuna zuriyarsu ta sarauta,matasa da manya suna shiga don tabbatar da cewa an kiyaye al'ada ta tsararraki.
A yayin da ake gudanar da bikin, duk mahaya dawakai za su nufo wurin kallo suna daga hannu suna ta kirari da taken“Ranka ya Dede” cikin alfahari za su fita filin fareti.
Filin fareti zai cika da karar ganguna na gargajiya da kururuwar masu busa ƙaho, masu wasan motsa jiki ma suna halartar wannan biki wato Acrobat kenan za su taho suna jujjuyawa suna kama juna,hatta masu wasa da wuta.
Yayin da mawaƙa da mayaƙa da ke kan dawakan su,masu sulke ma ba a barsu a baya ba a filin faretin. Sa’ad da ɗaruruwan mahaya dawakai suke filin faretin,za a hango jerin gwanon Sarki daga tsakiya, har da masu gadinsa, ’ya’yansa, matansa, da raƙumar sa.
Miye kuka fi so dangane da wannan kayataccen biki na hawan DURBAR a ksar Hausa.