Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ki amincewa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna wadda ta yanke ranar Laraba,bisa tube shi daga kujerar mulki tare da bayyana dan takarar jam’iyyar adawa ta APC Nasir Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
A wani taron manema labarai da ya yi da yammacin Laraba,Yusuf ya ce bisa ga ra’ayoyin da tawagar lauyoyinsa suka bayar, hukuncin ya fuskanci kurakurai da rashin amfani da doka, don haka zai nemi shari’a a kotun daukaka kara.
Bisa yadda kotun ta cire Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) bayan ta ci kuri’u 165,663 daga cikin kuri’un da ya samu a lokacin zaben.
Alkalan da suka kunshi mutane uku karkashin jagorancin Oluyemi Asadebay sun yanke hukuncin cewa ba hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tantance kuri’un da ke kunshe da kuri’un ba.
Duk da hukuncin kotun,Yusuf zai ci gaba da rike mukamin har sai kotun daukaka kara kuma watakila kotun kolin ta yanke hukunci na karshe kan lamarin.
Kamar yadda Abba Kabir yayi jawabi bayan wannan yanke hukunci, inda yayi yabo ga Allah madaukakin sarki ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano na gari.
Yayinda yake musu tunin akan cewa “a ranar 18 ga Maris, 2023, kun fito cikin jama’a kun zabe ni a matsayin Gwamnanku da kuri’u 1,019,602 da tazarar kuri’u 128,897 tsakanin kaskancina da na biyu”
Ya cigaba da bayanin cewa, “an rantsar da ni a matsayin zababben Gwamnan ku a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 hakan yayi sanadin jam’iyyar da ta fadi zabe ta kai mu kotu.
Sai gashi bayan shafe kusan watanni shida ana shari’a a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a yau Laraba 20 ga Satumba, 2023 alkalan kotun sun yanke hukuncin nasu”.
kotun daukaka kara kuma watakila kotun kolin ta yanke hukunci na karshe kan lamarin.
“Kamar yadda ’yan Adam hukuncinsu na iya zama ba cikakke ba, akwai kurakurai da rashin amfani da doka kamar yadda kungiyar lauyoyinmu ta nuna.
Shi ya sa tsarin mulkinmu ya tanadi wasu matakai da za a ci gaba da su kamar Kotun daukaka kara da Kotun Koli.
“A kan wannan batu, mun riga mun umurci kungiyar lauyoyin mu da ta daukaka kara kan wannan hukunci da wuri-wuri don ganin an yi adalci.
Don haka bari in yi kira ga dukkan mutanen jihar Kano nagari da su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da bin doka da oda.
“Kada mutane su dauki doka a hannunsu,an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a fadin jihar.
“Wannan gwamnati za ta ci gaba da kokarin aikin ci gaban jihar mu bisa alkawuran da muka dauka, na neman kuri’u. Muna so mu tabbatar muku da cewa hakan ba zai sa mu sanyin gwiwa ba.
Haka kuma ba za ta yi mana kasa a gwiwa ba domin wannan koma baya ne na wucin gadi ga jihar mu da yardar Allah SWT.
“Yayin da nake godiya ga al’ummar Jihar Kano bisa goyon baya da addu’o’i da suke yi,zan yi amfani da wannan damar wajen yin kira garesu da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da tabbatar da cewa za mu samu adalci a kotunan daukaka kara.
Kana kuma ina mai tabbatar muku cewa za mu samu adalci a kotun daukaka kara kuma za a mayar mana da martabanmu Insha Allahu”.duk a cikin jawabin Gwamna Abba Kabir Yusuf.