هل ترغب في تلقي إشعارات بشأن آخر التحديثات للعناوين التالية؟

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Sa Himma Wajen Bunkasa Ilimi Cikin Gaggawa

بواسطة Hauwa Aliyu Balasa 21 سبتمبر 2023 0
A cewar Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq samar da ingantaccen ilimi ga miliyoyin yaran da ke bukatarsa shine kan gaba a yanzu ga kasashen duniya da kungiyoyin bayar da tallafi da abokan huldar ci gaba. Da yake jawabi a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2023 a birnin New York, AbdulRazaq ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe kudade dayewa wajen samar da ababen more rayuwa a makarantu. Ya  kuma bullo da fasahar kere-kere domin inganta dabarun koyarwa, da rikon sakainar kashi, da ingantaccen koyo wanda ke baiwa yara dama. su kasance daidai da takwarorinsu a wasu lokuta. A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai Rafiu Ajakaye ya fitar ya ce, "Abin da muka yi ya baiwa malamai damar bin ka'idojin karatu na taimakawa yara su koyi karatu da rage rashin zuwa makaranta, da kuma kara yawan shiga makarantu bisa kaida. Gwamnan ya ce bangaren ilimi da ke da kudade mai kyau kuma yana rike da mabudin ci gaba a bangarori da dama kamar kiwon lafiya, ruwa, ci gaban biranen karkara da samar da abinci. Inda ya kara da cewa bayanan da aka dauka  na daga makarantu na iya taimakawa gwamnatoci wajen yanke shawara mai kyau. Abdulrazaq ya kara da cewa, an inganta makarantun gwamnati da kusan kashi 48.7% a matakin farko, yayin da bullo da fasaha ya karawa malamanmu da yaranmu karfi, ko da yake ya ce har yanzu tallafin kudi ya kasance babban kalubale. Ya yi bayanin cewa karancin karatu a makarantun gwamnatin jihar Kwara ya ragu daga kashi 70.8% zuwa kashi 51.6 cikin dari a cikin sati 40 da bullo da sabon shirin na KWARALEARN. Banda jihar Kwara ya kamata sauran jihohin Najeriya su samu irin wannan cigaba ta hanyar siyasa da kuma dabarun dogaro da kai don samar da ilimi ga kowa da kowa da kuma kyakkyawan sakamakon koyo ga matasa.

المزيد من المقالات

تحميل المزيد...

يسلط الضوء

قصة مميزة

التحريري

أعمدة

Menu