Apakah Anda ingin menerima pemberitahuan tentang pembaruan terkini dari berita utama berikut?

Da Dumi-Dumi: Keyamo Ya Kaddamar Da Dabarun Hanyoyin Masana'antar Sufurin Jiragen Sama

Oleh Hauwa Aliyu Balasa 13 September 2023 0
Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo, ya kaddamar da taswirori guda uku na harkar sufurin jiragen sama a Najeriya. Hakan ya zo ne yayin da ya nemi afuwar kamfanonin jiragen sama na kasashen waje kan kudaden da suka makale kuma suka haddasa rikici a wannan fannin a Najeriya kusan shekaru biyu. Lokacin da yake jawabi a wajen taron sufurin jiragen sama karo na 7, wanda ya gudana a Abuja ranar Laraba, Keyamo ya ce,kiyaye dokoki, kula,gyara, bada hayar jirgin sama a matsayin wasu abubuwan da gwamnatin ta sa a gaba. Ya kuma yi bayanin cewa su ukun na da matukar muhimmanci ga ci gaban harkar sufurin jiragen sama. Ya koka da cewa abin kunya ne ga daukacin kasashen yammacin Afirka rashin samun kayayyakin aikin MRO na duniya, amma ya ba da tabbacin cewa kasar za ta jagoranci hakan. Ministan ya kuma nuna rashin jin dadinsa da makudan kudade na kamfanonin jiragen sama na kasashen waje a Najeriya. Sauran bayanai zasu biyo baya

Artikel Lainnya

Muat lebih banyak...

Menu