Le gustaría recibir notificaciones sobre las últimas actualizaciones de los siguientes titulares?

Harkokin Tsaro:birtaniya Ta Kawo Tallafi Ga Tekun Najeriya

Oleh Hauwa Aliyu Balasa 11 de septiembre de 2023 0
A ranar Lahadi ne jirgin ruwan yaki na Royal Navy HMS Trent ya isa birnin Lagos Najeriya. Wannan ziyarar ita ce ta biyu da Trent ke kai wa Najeriya, a matsayin wani bangare na aikinta,da kuma yankin ta na taimakon kawayenta da abokan hadin gwiwa wajen dakile ayyukan ta'addanci kamar fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi. A cewar wata sanarwa da babbar hukumar Biritaniya ta fitar, ziyarar za ta taimaka wajen ba da horo da kuma tallafawa harkokin tsaron teku a yankin. Hukumar ta ce jirgin ya tashi daga Gibraltar dauke da kwararrun tawagar jiragen ruwa na Birtaniya Royal Marines da kuma wani jirgin sa ido maras matuki na Puma. Yayin da ya kara da cewa, “Aikin HMS Trent shi ne tallafi zuwa ga kasashen yammacin Afirka da kuma goyon baya zuwa ga kasashe wajen bunkasa karfin yaki da laifuka a teku,ya kuma bada tabbaccin cewa za su iya. Bugu da kari kuma suna taka rawar gani wajen samar da kwanciyar hankali a yammacin Afirka."Tare da kusan fam biliyan 6 na kasuwancin Burtaniya da ke ratsa yankin. Wani bangare na aikin Trent shi ne taimako wajen samar da kwanciyar hankali a gabar tekun Guinea ta hanyar horarwa don goyon bayan sojojin ruwa da hadin gwiwa bisa yaki da masu aikata laifuka, inganta alaka da musayar ilimi, yayin da suke gudanar da sintiri don karuwan tsaro." Kwamandan rundunar HMS Trent, Kwamanda Tim Langford, ya ce, “Rundunar Sojin Ruwa na da dadadden tarihi a cikin yankin da kuma hadin gwiwa mai dorewa da Sojojin Najeriya. Mataimakin babban kwamishinan Burtaniya a Legas, Jonny Baxter, ya ce tura sojojin ya nuna yadda da gaske duniya ta Biritaniya ke tashi a fagen duniya don tunkarar kalubalen tsaro na kasa da kasa. A cikin abunda ya Lura dasu shine  “Nijeriya muhimmiyar abokiyar tsaro ce mai daraja ga Burtaniya a yammacin Afirka. Kuma Kasashen namu biyu suna fuskantar barazana iri-iri shiyasa muke sha'awar yin aiki tare da Najeriya don murkushe wadannan da kuma taimakawa wajen inganta tsaron teku a mashigin tekun Guinea."

Más artículos

Carga más...

Menu