Tsadar rayuwa da kasar Najeria take ciki ya sa Jami'ar Bayero dake Kano (BUK) ta shirya tallafawa ma'aikata da ɗalibanta wajen rabon Kayan Tallafi domin rage musu zafi da radadin da ake Fama dashi a kasar gameda cire tallafin man fetur, Hukumar Jami’ar BUK zata kuma Samar da motoci na jigilar dalibai,hakan zai sa su Kara samun saukin Rayuwa da kuma tafiyar da karatun su bisa tsari.
Shugaban jami'ar, Farfesa Sagir Abbas,ya bayyana hakan ne a taron jami'ar karo na 56 da aka gudanar ranar 22 ga watan Yulin 2023, kana kuma Kakakin Jami’ar BUK ,Garba ya bayyana cewa jami'ar ta cire wa ma’aikata 500 da suke zama a rukunin gidajen jami’ar biyan kuɗin wutar lantarki da ruwa. Yayinda ya kara da bayanin dalilin da yasa ba a cire musu biyan kudin gaya ba inda ya ce Kai tsaye ake biya zuwa asusun ma’aikatar ilimi.
Tsadar rayuwa da kasar Najeria take ciki ya sa Jami'ar Bayero dake Kano (BUK) ta shirya tallafawa ma'aikata da ɗalibanta wajen rabon Kayan Tallafi domin rage musu zafi da radadin da ake Fama dashi a kasar gameda cire tallafin man fetur, Hukumar Jami’ar BUK zata kuma Samar da motoci na jigilar dalibai,hakan zai sa su Kara samun saukin Rayuwa da kuma tafiyar da karatun su bisa tsari.Shugaban jami'ar, Farfesa Sagir Abbas,ya bayyana hakan ne a taron jami'ar karo na 56 da aka gudanar ranar 22 ga watan Yulin 2023, kana kuma Kakakin Jami’ar BUK ,Garba ya bayyana cewa jami'ar ta cire wa ma’aikata 500 da suke zama a rukunin gidajen jami’ar biyan kuɗin wutar lantarki da ruwa. Yayinda ya kara da bayanin dalilin da yasa ba a cire musu biyan kudin gaya ba inda ya ce Kai tsaye ake biya zuwa asusun ma’aikatar ilimi
Ya kuma kara da cewa ƙaramin bankin jami'ar na kokarin samar da bashi mara ruwa ga ma'aikata domin wannan zai basu damar biyan kuɗin makarantar yayansu.